Matan Gwamnonin Arewacin Najeriya sun yi kira ga jami'an tsaro a jihohin da aka kafa dokar-ta-baci su kare hakkin al'umma
WASHINGTON, DC —
Matan gwamnonin arewacin Najeriya goma sha tara sun yi alkawarin tallafawa iyalai a jihohin da aka kafa dokar-ta-baci.
Matan sun bayyana haka ne a wani taron da suka yi a Minna fadar gwamnatin jihar Naija da nufin tallafawa yunkurin gwamnati na wanzar da zaman lafiya a jihohin yankin musamman jihohin da aka kafa dokar –ta- baci.
Matan gwamnonin sun kuma yi kira ga jami’an tsaron da aka tura jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa suyi kyakkyawan kula yayin gudanar da ayyukansu domin kada su sake jefa al’umma cikin halin kunci.

Your browser doesn’t support HTML5