Wani kakakin soja, yace ana kai farmaki a kan dukkan sansanonin da ake kyautata zaton na 'yan bindiga ne a dukkan jihohi uku da aka ayyana kafa dokar-ta-baci a yankin arewa maso gabashin kasar. Kakakin yace an ragargaza ko kuma an kwace sansanoni da dama a Jihar Borno.
Birgediya-janar Chris Olukolade ya fada yau jumma'a cewa an kashe 'yan tawayen da ba a san adadinsu ba a wadannan nhare-hare da aka kai da jiragen yaki da helkwaftoci na kai farmaki.
Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana kafa dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa ranar talata, a bayan da kungiyar Boko Haram ta zafafa irin hare-haren da take kaiwa a yankin.
A halin da ake ciki kuma, 'yan rajin kare hakkin bil Adama na Najeriya, su na yin marhabin da jan kunnen da gwamnatin Amurka ta yi ma hukumomin Najeriya da su guji yin amfani da karfi fiye da kima a yunkurinsu na takalar 'yan kungiyar Boko Haram. Auwal Musa Rafsanjani, ya bayyana dalilansu na goyon bayan wannan gargadi daga Amurka: