Matan da suka sha taba sigari suna cikin hadarin kamuwa da sankaran nono

Wani jami'in Binciken kwakwa.

Wani sabon bincike na nuni da cewa, matan da suka daina al’ada wadanda suke shan taba sigari, ko suka taba sha a can baya, sun fi fuskantar kasadar kamuwa da cutar sankarar nono

Wani sabon bincike na nuni da cewa, matan da suka daina al’ada wadanda suke shan taba sigari, ko suka taba sha a can baya, sun fi fuskantar kasadar kamuwa da cutar sankarar nono. Masu bincike na Amurka ne suka gudanar da wannan binciken da aka wallafa a mujallar aikin jinya ta kasar Birtaniya da ake kira British Medical Journal. An yi nazari kan rayuwar Amurkawa mata dubu tamanin tsakanin ‘yan shekaru hamsin zuwa saba’in da tara. Binciken ya yi nuni da cewa, wadanda suka sha taba sigari suna fuskantar karin kasadar kamuwa da cutar sankarar nono da kimanin kashi goma sha shida cikin dari fiye da matan da ba su taba shan taba ba. Matan da suka sha taba amma suka daina, har yanzu suna fuskantar karin kasadar kamuwa da cutar da kimanin kashi tara bisa dari. Binciken ya kuma ce, matan da suka daina al’ada dake shakar hayakin taba na lokaci mai tsawo su ma su na iya fuskantar karin kasadar kamuwa da cutar sankarar nono. Kwararru a fannin aikin magani sun jima su na mahawara kan dangantakar shan taba sigari da cutar sankarar nono, inda aka rika samun sabanin sakamako a bincike dabam dabam da aka gudanar.