Matakin Takaita Tafiye-tafiyen Jami'an Diflomasiyar Pakistan Da Amurka Ta Dauka Ya Fara Aiki Yau

Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amurka

Amurka ta mayarwa Pakistan martani saboda daga yau an takaita tafiye-tafiyen jami'an diflomasiyar kasar dake nan Amurka

Daga yau Jumaa ne Amurka ta takaita wa jamiaan Diflomasiyyar kasar Pakistan yin tafiye tafiye, kamar yadda jakadar kasar Aizaz Chaudhry ya fada wa wannan gidan radiyon.

Yana cewa a nawa ra’ayin wannan shawarar ta sabawa dokar kasa da kasa, Ambasadan yayi wannan furucin ne sailin da yake magana da sasshen Urdu na wannan gidan Radiyon, yace kamata yayi kasashen biyu su kusanci juna, amma daukar mataki irin wannan ba zai haifar da kyakkyawar sakamako ba daga karshe.

Sai dai a waje daya maaikatar harkokin wajen na Amurka na cewa bata da wani bayani da zatayi game da wannan lamari, domin ko tun farko tace tana da ikon kakaba wasu sharuddan dake da nasaba da tafiye-tafiye, a karkashindokar tafiya ta shekarar 1982.

Sai dai Ambasada Chaudhry yace ga bisa dukkan alamu akwai wata boyayya a cikin wannan shawarar ta Amurka