Matakin mayar da kasar Mali saniyar ware a sahun kasashen yammacin Afrika sakamakon rashin nuna alamun shirya zaben da zai mayar da mulki a hannun farar hula abu ne da masana ke ganin ba zai hafar da da mai ido ba a fannin tsaro a yankin Sahel, ganin cewa rufe iyakokin kasar da makwaftanta ka iya zama wani shinge ga dakarun tsaro a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’adda kamar yadda mai fashin baki a fannin tsaro Alkassoum Abdourhaman ya bayyana.
Editan jaridar l’evenement jami’i a cibiyar nazari da bincike ta Nobert, Zango Moussa Aksar na cewa shugabanin kasashen CEDEAO ba su yi la’akari da abinda zai biyo baya ba kafin yanke hukunci akan kasar Mali.
Ku Duba Wannan Ma ECOWAS Na Shirin Gudanar Da Babban Taron Gaggawa Game Da Juyin Mulkin GuineaMakwabciyar Mali wato kasar Aljeriya, wacce ba ta cikin kungiyar ECOWAS ta yi tayin sulhu ga bangarorin biyu, Masana sun yaba da wannan dattako na Aljeriya.
Sanannen abu ne cewa matsalar tsaron da ta addabi yankin Sahel shekara da shekaru wani abu ne da ya samo tushe daga yanayin da ake ciki a arewacin Kasar Mali, yankin da kungiyoyin ta’addanci suka mayar da shi matattara wanda kuma ke ba su damar tsallakawa Nijer da Burkina Faso yayin da sannu a hankali abin ya fara danganawa zuwa iyakokin jamhuriyar Benin da Cote d’ivoire.
Saurari Rahoton Sule Mumuni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5