Matakin Jingine Zaben 'Yan Niger Mazauna Waje Na Tayar Da Kura

Hukumar Zabe a Niger

Kotun tsarin mulkin jamhuriyar Nijer ta fitar da sanarwa a game da ce-ce ku-cen da ya barke bayan da gwamnatin kasar da hukumar zabe ta CENI suka bukaci ta fayyace masu matsayin doka a game da matakin da ake shirin dauka don jingine zaben ‘yan nijer mazauna kasashen waje sanadiyar annobar coronavirus.

Tuni ‘yan siyasa da ‘yan rajin kare demokaradiya suka fara tofa albarkacin bakinsu akan sanarwar kotu.

A sanarwar mai dauke da sa hannun shugabanta mai shari’a Bouba Mahamane, kotun tsarin mulkin Nijer ta bayyana cewa ana iya daukar anobar cutar corona a matsayin wata babbar matsala da ka iya haddasa cikas a sha’anin gudanar da zabe.

Ta kuma ce rashin yiwa ‘yan Nijer mazauna ketare rajista saboda irin wannan dalili ba zai shafi halaccin kundin rajistar kasar ba to amma ya danganta da yadda hukumar zabe ke tafiyar da ayyukanta na tsara zabe.

Sakataren watsa labaran jam’iyar PNDS Tarayya Boubacar Sabo ya bayyana cewa, sanarwar kotun ta kawo karshen duk wani ce-ce ku-ce akan zaben kasashen waje.

Sai dai masu rajin kare demokaradiya na ganin dole ne bangarorin siyasa su sulhunta da juna ta yadda za a gudanar da zabe cikin nutsuwa.

A nan gaba ne ake sa ran ‘yan adawa zasu bayyana matsayinsu akan wannan lamari da ke wakana a wani lokacin da ya rage watannin 5 a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Matakin Hana 'Yan Niger Mazauna Kasashen Waje Zabe Na Tayar Da Kura