Abokin aiki na sashen turanci a nan Muryar Amurka Clottey Peter ya zanta da wani babban jami'in dake shugabancin kwamitin dake yaki da cutar ebola a kasar ta Saliyo.
Yayin da suke zantawa jami'in yace ko ba komi mutanen kasar sun kara samun fahimta akan cutar. An samu karin mutane da suka kira suna bayyana kansu a matsayin wadanda suke fama da cutar. A ranar farko fiye da mutane dari shida suka bayyana kansu. A rana ta biyu an samu fiye da mutane 1600 da suka fito.
Yayin da mutane ke zaune cikin gidajensu jami'an kiwon lafiya dubu talatin aka baza a duk fadin kasar. Jami'an sun gano gawarwaki casa'in wadanda suka mutu sanadiyar cutar.
Jami'in yace gwamnati bata dauka cewa hana mutane fita na tsawon kwana uku shi zai kawo karshen cutar ba amma ya bude masu wani babi da kuma taimaka masu wayar da kawunan mutane akan tsafta da kuma samun damar kafa wuraren jinya da ba'a taba tunanen za'a iya samu ba.
Akan tsafta yace a wata anguwa kawai sun raba sabulu fiye da dubu dari biyu. Sun kafa wurin jinya masu gadajen kwana da dama tare da samun izinin yin anfani da wani sansani na 'yansanda.
Akan zargin da aka yi cewa an kaiwa wasu jami'an kiwon lafiya hari jami'in yace bashi da labari. Yace suna da kungiyoyin al'umma da wasu da suke zaman kansu da suka taimaka a wannan yakin. Idan da an kai ma wasu hari da sun fada.
Yayin da suke aikin zagayawa yace suna taro sau biyu kowace rana domin su tara bayyanai su kuma san inda aka kwana. Duk wannan ya basu zarafin sanin inda aka kwana da batun yaduwar cutar ta ebola a kasar
Daga karshe jami'in yace daratsin da suka koya da abubuwan da suka gano zasu taimaka wurin sanin matakan da za'a dauka nan gaba.