Wasu sabbin bayanai da hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ta kididdige, sun nuna cewa tsauraran matakan da ake dauka na ruguza kungiyar IS a Afghanistan, na samun nasara a wasu yankunan kasar, sai dai kuma duk da haka, an gaza kawar da tushen kungiyar baki daya a kasar.
An yi kiyasin cewa, reshen kungiyar IS na Khorasan na da mayaka sama da dubu daya, wadanda aksarinsu ke kudancin Lardin Nangarhar, inda wani adadi kadan daga cikinsu ke gudanar da ayyukansu a gabashin Lardin Kunar da ke kasar.
Daga cikin wadanda suke ci gaba da mubaya’a ga kungiyar ta IS mai da alama mai bakar tuta, akwai ‘yan kasar ta Afghanistan da wasu mayaka daga Pakistan da Uzbekistan, a cewar wani babban jami’in yaki da ayyukan ta’addanci yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka.
Ya kara da cewa an yi ammanar cewa, wasu mayakan reshen kungiyar ta IS na Khorasan na kai hare-hare a Pakistan.
Yayin da jami’an tsaro da na tattara bayanan sirri a Amurka ke gargadin cewa ya kamata a yi hattara da adadin mayakan, lura da cewa, kididdigar mayaka ‘yan ta’adda, ta sha banban da yadda kimiyya ke fayyace abu, adadin ya nuna cewa reshen kungiyar IS na Khorasan, na kirkiro da dabarun kaucewa yunkurin da Amurka ke yi na kawar da kungiyar ta IS.