Matakan Hana Barin Ciki

Yarinya ta taba cikin uwa

Masana sun ce barin cikin mata ba abin da za a iya hanawa ba ne, musamman mata masu ciki da ba su kai wata uku ba
Masana sun ce barin cikin mata ba abin da za a iya hanawa ba ne, musamman mata masu ciki da ba su kai wata uku ba. Sun kuma ce, ba lalai a iya sanin asalin dalilin da yasa wadansu mata suke yin barin ciki ba.

Doctor Amina Umar Makarfi ce ta asibitin koyarwa na jammmi'ar Ahmadu Bello ta bayyanà haka wurin wani taron lafiya da kungiyar mata Musulmi a jihar Kaduna ta shirya.

Doctor Amina ta bayyana cewa, ana iya gano dalilin zubar da ciki wani lokaci, idan mace mai cikin tana zuwa awo aka kuma san irin damuwa ko matsala da takeda ita.

Tace matan da suka yi bari suna iya samun matsalar haihuwa bayan barin. Yawancin lokaci, idan ba a lura da barin ciki ba, har kwayoyin cuta suka shiga ma’haifa, mace za ta iya samun matsalar haihuwa.

Idan mace tayi barin ciki har ta yi ta zubar da jini, bata sami kulawa yadda ya kamata ba tana iya mutuwa. Saboda haka ake karfafa mata su rika zuwa asibiti a duba lafiyarsu lokacin da suke da ciki.

Doctor Amina tayi karin haskea hirarsu da wakilin Sashen Hausa Nasiru Yakubu Birninyero

Your browser doesn’t support HTML5

Matakan hana barin ciki - 2:09