Matakan Da Aka Dauka Na Tantance Matasa Sama Da Dubu 900,000 Masu Neman Shiga Aikin Dan'Sanda -inji Sanata Abu Ibrahim

Shugaban Kwamitin kula da Aikin ‘Yan sanda Sanata Abu Ibrahim ya yi bayanin matakan da aka fara dauka domin tanttance matasa sama da dubu dari tara da suka cika takardun neman aiki ta yanar gizo.

A wata hira ta mussamman da yayi da Muryar Amurka, Sanata Abu Ibrahim ya ce ba magudi, ba sani ba sabo a tanttancewar, saboda anyi amfani da wata na'ura ce ta musamman.

Shugaban ya kara da cewa akwai maganar shekaru, wanda yake neman shiga matakin karabiti zai kasance daga shekara 25 ne zuwa kasa, ofisa da sufeto kuma shekaru 28, dan haka duk wanda ya wuce wadannan shekaru to lallai za’a cire sunan sa.

Na uku akwai maganar tsayi, idan tsayin wanda yake neman aikin bai kai mizanin da ake bukata ba lallai za’a cire shi domin haka ka’idar aikin ta tanadar, kuma shakka babu sune wadanda kwamfuta ta cire daga cikin jerin sunayen da suka cika wanna takarda ta neman aiki.

Sanatan ya kara da cewa yanzu maganar kabilanci ko siyasa ko addini ta kare, can-canta ake bi domin haka ba sani ba sabo, ko daga ina mutum yake idan ya can-canta babu abin da zai hana a dauke shi wannan aiki.

Daga karshe ya yi Karin bayanin cewa kowacce karamar hukuma za’a dauki mutane tara ne a matakin karabiti, a matakin sufeta da ASP kuma kowace jaha za’a ba mutane goma sha biyu ne.

Ga cikakkiyar hirar.