Tarihin wasan fadan “Boxing” bazai cika ba, har sai an anbaci dan Najeriya Anthony Joshua, wanda ya samu damar kwace kambun dan wasa da yafi karki a fagen wasan boksin a kasar ingila, na duniya.
Anthony, mai shekaru ashirin da tara 29, ya samu nasarar daukar wannan kambu ne, bayan wasannin goma sha shida da ya buga. Buge dan wasa Martin, da yayi da faduwa biyu, tasa ya zama gwarzo, a fagen wasan boksin. A dai-dai lokacin da suke gwabzawa da Martin, dan asalin kasar Amurka, ya buge shi har sau biyu, cikin minti daya da dakikoki kadan sai yayi nasara.
Wasu masu sharhi a fagen wasan boksin, dai na ganin cewar Anthony, yaro ne mai zafin nama da zai yi wuya a samu wanda zai iya bashi kashi. Harma wasu na bayyanar da kwazon shi kamar na margayi Muhammad Ali, na kasar Amurka da yayi tashe a shekaru da dama da suka gabata. Yanzu haka dai Najeriya, na rike da wannan kambu na wanda yafi karfi a duniya na kungiyar “IBF world heavyweight title.”