Ko da yake, jim kadan, mataimakiyar firai minister Ukraine Irina Vereschuk, ta yi watsi da wa’adin. Ta shedawa tashar yada labarai Pravda ta Ukraine cewa, “Ba za’a yi maganar mika wuya da ajiye makamai ba. Mun riga mun sanar da bangaren Rasha game da wannan.”
A cewar kamfanin dillanci yada labaran kasar Rasha RIA, ma’aikatar tsaron Rasha ta bukaci amsa daga sojojin Ukraine da karfe biyar na safe agogon Moscow wato karfe 4 ke nan agogon Kyiv. Moscow ta yi nuni da kin mika wuya ga yin sulhu a matsayin ra’ayi ne da “yan bindiga.”
Wa’adin yana zuwa ne sa’o’i bayan da Zelenskyy ya shedawa Fareed Zakaria na gidan talabijin CNN a wata hira da aka watsa jiya Lahadi cewa, rashin cimma yarjejeniya tare da Rasha “Zai iya nuna cewa wannan yakin duniya na uku ne.”
Zelenskyy ya yi kira da a gudanar da cikakkiyar tattaunawar zaman lafiya da Moscow, wadda za ta maido da martabar yankuna da kuma samar da adalci ga Ukraine.
Jagoran masu shiga tsakanin na Rasha ya ce a cikin ‘yan kwanakin nan bangarorin sun matsa kusa da cimma matsaya kan batun Ukraine ta yi watsi da yunkurinta na shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO da daukar matsayi na tsaka tsaki.
Zelenskyy ya shedawa CNN cewa sojojin Rasha sun shiga Ukraine “domin su hallaka mu, su kashe mu,” amma ya sha alwashin cewa Ukraine ba za ta amince da mika diyaucinta ko yankunanta ba.