Mataimakin shugaban Kasar Amurka Mike Pence ya isa Alkahira yau asabar, inda zai tattauna shugaba Abdel fatah El-sisia kan batutuwan da suka shafi tsaro, taadanci,ciki ko harda batun yaki da kungiyar IS.
Dama tun a cikin watan December ne aka shirya wannan ziyarar amma kasancewar mataimakin shugaban kasan cikin batun tattaunwa game da sabon tsarin harajin kasa da ake son ayiwa kwaskwarima da kuma kin ganawar da shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas yaki na ya amince ya gana dashi a Bethlehem yasa aka dage ziyarar.
Shugaban na Falesdinawa yayi fatali da shawarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na cewa ya amince da birnin kudus a matsayin fadar gwamnatin Israela.
Pence dai shine babban jamiin gwamnatin Amurka na farko yakai ziyara a kasashen Gabas ta tsakiya tun bayan lokacin da Shugaba Trump ya bayyana birnin kudus a matsayin fadar Izraila.
A cikin sanarwan da, White House ta fitar tace wannan ziyarar ta mataimakin shugaban kasa ya kara jaddada manufar Amurka ne nayin aiki da kawayen ta wajen ganin an yaki mumunar akidar dake zamewa barazana ga matasa masu tasowa nan gaba.
Birnin Alkahira dai shine zango na farko da mataimakin shugaban kasar ya yada zango a wannan ziyarar tasa ta kwanaki hudu a kasahen da suka hada da Jordan da kuma Izraila.
Sai dai ba asa rai mataimakin shugaban kasar ya gana da shugaba Falesdinawa