Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Kai Ziyara Yankin Numan

Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Najeriya

Mataimakin shugaban kasan Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya na jihar Adamawa, don ganewa idanuwansa halin da ake ciki game da rikicin da ya auku a yankin Numan dake kudancin jihar a tsakanin al’umman Bachama da Fulani Makiyaya.

A dai dai lokacin da aka kara baza jami’an tsaro a yankin Numan dake kudancin jihar Adamawa biyo bayan tashin hankali da ya auku a yankin dake da nasaba da fadar kabilanci a tsakanin al’ummar Bachama da kuma Fulani makiyaya lamarin da ya jawo asarar rayuka,yanzu haka shugabanin al’umma a yankin na kiran a yafewa juna,kowa ya maida wuka cikin kube.

Wannan rikici dai, baya ga asarar rayuka, da dukiya, yanzu haka na neman maida yankin na Numan kufayi sakamakon gudun hijiran da ake yi.

To sai dai kuma yayin da hankula ke fara kwantawa,shugaban karamar hukumar ta Numan Rabaran Arnold Jibila wanda ya tabbatar da cewa kauyuka takwas abun ya shafa,yace yanzu haka tuni suka soma daukar matakin gano bakin zaren magance tashin hankalin.

Koda yake ya zuwa yanzu ba’a bayyana adadin wadanda aka kashe ba, amma rahotani na cewa rayuka da dama ne suka salwanta ciki har da na wasu hakimai biyu, yayin da bayanan da ba’a tabbatar ba ke cewa wasu gungun matasa sun tare hanyar Sabana suna kisan daukar fansa, kuma wannan ma na ko zuwa ne yayin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ke kawo ziyarar gani da ido a garin na Numan a yau Talata.

Yanzu haka dai tuni wasu kungiyoyin matasan Bachama suka yunkuro domin kawo fahimtar juna a yankin kamar yadda ,daya daga cikin shugabanin matasan yankin Afraimu Paul Turaki ya bayyanawa manema labarai.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Kia Ziyara Numan - 3' 07"