Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Sabon Shirin RUGA A Adamawa

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya A Adamawa

Yayin da ake cigaba da cece-kuce game da sabon shirin Ruga da gwamnatin Najeriya ta kuduri aniyar aiwatarwa da aka dakatar, yanzu haka gwamnatin kasar ta soma kaddamar da wani sabon shiri na tada komadar makiyaya ta.

An dai soma kaddamar da shirin ne a jihar Adamawa, Arewa Maso Gabashin Najeriya, inda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yaje ya kaddamar.

Da yake kaddamar da shirin a gandun kiwo na Gongoshi, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, yace manufar shirin daban yake da shirin Ruga da ake ta cece-kuce akai. An kaddamar da shirin ne domin magance tashe tashen hankulan dake wakana tsakanin makiyaya, da manoma.

Yace yanzu kusan jihohi bakwai ne suka rungumi wannan shirin da suka hada da Adamawa, Benue, da Kaduna, Filato, Nasarawa, Taraba, da kuma jihar Zamfara.

Shiko mai masaukin baki gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri yayi amanar cewa shirin zai kawo cigaba ta fannin zaman lafiya, da bunkasa kiwo na zamani, da kuma samar da fahimtar juna.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Sabon Shirin RUGA A Adamawa



.