Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Da Wasu 9 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Sama

Le vice-président du Malawi, Saulos Chilima, s'exprime lors d'une conférence de presse dans sa résidence, Lilongwe, le 5 février 2020.

Mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Chilima, ya mutu a wani hatsarin jirgin sama, kamar yadda shugaban kasar ya bayyana a ranar Talata, bayan da masu bincike suka gano tarkacen jirgin a wani dajin da ke cike da hazo.

Jirgin sojan da ke dauke da Chilima mai shekaru 51 da kuma wasu 9 ya bace a ranar Litinin din da ta gabata, bayan da ya kasa sauka a birnin Mzuzu da ke arewacin kasar sakamakon mummunar yanayi, inda aka ce ya koma Lilongwe babban birnin kasar.

Hatsarin Jirgin Sama a Malawi

"Rundunar bincike da ceto sun gano jirgin inda gaba dayansa ya lalace ba tare da wani mai rai ba, saboda duk fasinjojin da ke cikin jirgin sun mutu sakamakon hatsarin," in ji shugaban Malawi Lazarus Chakwera yayin da yake jawabi ga al'ummar kasar.

Hatsarin Jirgin Sama a Malawi

"Kalmomi ba za su iya kwatanta irin takaicin wannan lamarin ba," in ji shi, yana mai bayyana hatsarin a matsayin "mummunan bala'i."

Plane crash

Hotunan da wani mamban tawagar sojojin da suka ceto ya raba wa AFP ya nuna jami'an soji a tsaye a kan wani tudu mai hazo kusa da tarkacen jirgin.

Kwamandan sojojin kasar Janar Paul Valentino Phiri, ya ce wasu kasashe da suka hada da makwabtan Malawi, sun taimaka wajen binciken, tare da tallafin da suka hada da jirage masu saukar ungulu da jirage marasa matuka.