Mataimakin Shugaban Amurka Zai Ziyarci Gabas Ta Tsakiya

Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence

Yau Juma’a mataimakin shugaban Amurka Mike Pence zai fara ziyara a Gabas ta tsakiya.

Mike Pence ne babban jami’i daga Amurka na farko da zai ziyarci yankin tun bayan sanarwar da Shugaba Donald Trump ya bada, na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, matakin da shugabannin duniya suka yi Allah wadai dashi.

Haka kuma Trump ya bada sanarwar Amurka za ta maida Ofishin jakadancinta zuwa birnin na Kudus daga birnin Tel Aviv. Ranar da aka yiwa lakabi da ranar fushi. Sannan zanga zangar nuna rashin amincewa da shawarar da Trump ta biyo bayan wannan sanarwa.

Ziyarar Pence ta kwanaki hudu ce kuma zata fara ne daga Misra da Jordan kafin ya wuce zuwa Isra’ila. Ba a zaton Pence zai hadu da shugabannin Falasdinawa.

Tunda farko an shirya Pence zai je yankin ne a watan Disamba, amma aka soke ziyarar sakamakon shawarar da Trump ya yanke akan amincewa da birnin Kudus a matsayin baban birnin kasar Isira’ila.