A hirar da yayi da Greta Van Susteren, wata mai bada tarbacce ga shirye-shiryen gidan rediyon nan na VOA a ofishinsa a jiya Laraba, yace, da farko ya kamata a san cewa Iran itace kan gaba wurin bada tallafi a ayyukan ta’addanci a duniya.
Yace, baicin zalunci da take hakkokin al’ummanta, Iran tana kuma aika yan ta’adda zuwa wasu kasashe dake yankin sannan kiuma m tana ci gaba da zama kasar dake da tasiri mai yawa da kuma hatsari a wannan yankin.
Sai dai kuma Pence yaki bada da karin bayani a kan matakan da Amurka ka iya dauka kan wannan lamari na Iran, yana mai cewar, akwai matakan bada taimako na musamman da Amurka da sauran kasashen duniya zasu iya baiwa mutane Iran, idan suka ci gaba da dagewa wajen neman yancinsu.