Mata Da Yara Na Cikin Hatsarin Rayuwa A Pakistan- Inji Ukumar UNICEF

Cibiyar Kula da Kananan Yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta ce a duk duniya, babu kasar da sababbin jarirai suke cikin hatsari kamar kasar Pakistan, inda daga cikin jarirai 1,000 da ake haihuwa, 46 suke mutuwa kafin su cika wata daya a duniya.

A cikin rahoton da ta sako kan wannan lamarin yau Talata, a matsayin wani bangare na kamfe din da take don a rika kula da jarirai a duniya, cibiyar ta UNICEF tace matan Pakistan masu ciki na fuskantar wahala wajen samun kulawa da yake duk mata 10,000 masu ciki, jami’an kiyon lafiya goma sha-hurhudu ne kawai ke iya basu kulawa.

Sai dai UNICEF ta kula da cewa a yanzu an sami karin matan dake zuwa asibiti suna haihuwa a kasar, inda abin ya cira daga kashi 21 cikin 100 zuwa kashi 48 ciki 100.