Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Yayi Kunnen Uwar Shegu Da Kiran Masana


Kamfanin Facebook ya yi kunnen uwar shegu da kira da masana suka yi masa, akan yunkurin sa na kirkirar manhajar sakon gaggawa ta zumunta ta yara, masana na ganin cewar wannan wani yunkuri ne da ba zai haifar da alkhairi ga cigaban yara ba.

Manhajar sakon gaggawar yara zata ba yara ‘yan shekaru kasa da 13, damar ganawa da iyayen su da sauran ‘yan uwan su a kowane hali da yanayi. Tsarin zai zo dauke da kariyayr tallace-tallace, kana iyayen yara zasu kayyade ma yara ire-iren abokai da dangi da suka kamata suyi mu’amala ta kusa a shafufukan.

Masana na ganin cewar wannan tsarin zai sa yara su zama sun kamu da cutar amfani da yanar gizo, wanda hakan ka iya haifar da wasu matsaloli da dama, ganin yadda wasu manya suke fuskantar matsalar amfani da shafufukan yanar gizo, balle ga yara.

Kamfanin dai na kara tallata manufofin sa dangane da sabuwar manhajar, da zummar cusa kaunar manhajar sakon gaggawa ta yara, ga iyaye da ma yara masu shekaru kasa da 13.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG