Masu Zanga-Zangar Bikin Addini A Nepal Sun Yi Arangama Da 'Yan Sanda
Your browser doesn’t support HTML5
Dubun-dubatar masu zanga-zanga sun yi arangama da ‘yan sandan kwantar da tarzoma, Alhamis, 3 ga Satumba, suna masu bijirewa kullen cutar coronavirus don gudanar da bikin addini a Nepal.
Masu zanga-zangar sun taru a garin Lalitpur a kewayen keken hawa mai mutum-mutumin gunkin Rato Machindranath.