A jiya litinin “yan sanda a birnin Washington su ka yi amfani da karfi wajen maida masu zanga-zanga baya yayin da suke kokarin sauke wani mutum-mutumin tsohon shugaban Amurka Andrew Jackson dake wani filin shakatawa kusa da fadar White House.
Masu zanga-zangar sun sakala wa mutum-mutumin dake wurin shakatawa na Lafayette igiya ne suna kokarin karyawa sai ‘yan sanda da yawa da ke kula da wuraren shakatawar suka yi amfani da kulake da abun barkonon tsohuwa su ka tarwatsa su.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi Allah wadai da halayyar masu zanga-zangar a shafinsa na twitter kuma ya gargade su da su yi hattara, ya kara da cewa "mutum zai iya fuskantar daurin shekaru 10 a gidan kaso karkashin dokar mutunta tunawa da yan mazan jiya."
Wannan wurin na kusa da inda a watan jiya aka tarwatsa masu zanga-zanga dab da fitowar shugaba Trump yayin da yayi tattaki domin daukar hoto a wata majami'a da ke tsallaken Lafayette.
Mutum-mutumin shugaban Amurka ne na 7 tsakanin 1829 zuwa 1837 sanye da kayan soja a bisa kan doki don karrama aikin soji da yayi kafin ya zama shugaban kasa.
Ana zarginsa da sa hanu a wata doka a 1830 data bada damar korar dubban kabilun Amurka daga gonakinsu a kudancin Amurka, al’amarin da aka yiwa lakabi da ‘The Trails of Tears” saboda da yawa sun mutu yayin da aka tunkuda su zuwa yammaci.