Wannan yarjejeniya ita ce irinta ta farko da Westbrook zai yi a Afrika. Karkashin wannan aikin hadin gwiwa, kamfanonin zasu fitar da fina finan kashi kashi guda biya kana da cikakken fim guda.
A cikin aikin akwai shirin barkwancin da aka yiwa take “Dada Safari” da aka shirya kashi kashi a kan Afrika. An gina labarin shirin ne a kan wasu aminan juna hudu da suka rasa mafita a rayuwa da wurin aiki, da suka shiga harkar daji bayan da daya a ciki ta gaji wani dadadden ginin masu daji na mijinta da aka mace dashi kana ta gayyaci abokanta zuwa sabon ginin da ka yiwa kwaskwarima da kuma aka sake bude kasuwanci.
A cikin shirin The Gods,” wasu ma’auratan farfesoshin jami’ar Cambridge sun shirya yin nazari ne a kan dalilin da yasa ake yawan samun bal’o’I daga Allah, amma a karshe suka gano wasu gumakan Afrika guda bakwai da aka mance dasu. Sun nemi taimakon wasu yara biyu ba su baiwa a Afrika da zasu tattauna sa wadannan gumaka, akwai rashin yiwuwar wannan rukunin masu binciken gano sirrin wannan gumaka dake raye a duniya kamar yanda suka san duniyar ta sauya har illa masha Allah.
Shiri na karshe shi ne "Are We Getting Married?” wani shirin barkwanci ne da aka shirya a Amurka da yake bada labarin ‘yar wasu hamshakan attaijira na Najeriya da suke soyayya da bakar fatar ba-Amurke daga Atlanta kana suka dau shawarar yin aure. Yayin da masoyar suke niyar shirya kwarya kwaryar buki, su ko iyayen su suna da wani tunani na daban, lamarin da ya kai masoyar ga daukar shawara ko su yi tsayin daka a kana bin da suke so ko kuma su amince da babban bukin Yarbawa a auren da za a yi a Atlanta wanda basu so.
Kamar yanda muka bayyana a watan day a gabata, fadadat da Westbrook ya samu a cikin wannan lokaciya hada da wata yarjejeniyar kasa da kasa da wani mai shirya fina finai a Isra’ila, Tedy Productions. EbonyLife Studios kuma a baya ya kulla yarjejeniya kamfanoni ciki hard a Netflix da kuma Sony Pictures TV.