Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kuduri Aniyar Yaki Da Matsalar Cin Zarafin Mata A Najeriya

Kungiyar CODE tare da shugabannin ofishin jakadancin kasar Canada

Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen bai wa mata damar fitowa su bayyana kowanne irin cin zarrafi su ke fuskanta  a rayuwa.

A yayin da ake ci gaba da neman mafita mai dorewa a game da matsalolin da suka shafi cin zarafin mata da kananan yara, kungiyar farar hula ta ‘’Connected Development’’ da hadin gwiwar ofishin jakadancin kasar Canada a Najeriya ta kaddamar da aikin wayar da kan al’umma, tare da rattaba hannu kan wata yarjejeniya aiki tare don kawo karshen matsalar mussaman a arewacin kasar.

Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen bai wa mata damar fitowa su bayyana kowanne irin cin zarrafi su ke fuskanta don tabbatar da samin al’umma na kwarai a daidai la'akari da wannan lokaci da ake cigaba da fuskantan kalubalen tsaro a sassan kasar daban-daban.

Shugaban Kungiyar ta CODE Hamzat Lawal ya bayyana cewa Kasar Canada ta bada tallafi ga kungiyar ta CODE don marawa tsarinta na horarwa da karfafa masu rajin tabbatar da yaki da matsalolin da suka shafi na jinsi a arewacin Najeriya

Kevin Toker dake zaman mukaddashin jakadan kasar Canada a Najeriya ya bayyana cewa daya daga cikin kudurorin gwamnatin kasarsa shi ne tabbatar da ba da taimako ga marasa karfi da ke bukatar a kare mu su hakkinsu na bil’adama musamman a bangare ci mu su zarrafi.

Kelvin Tokar tare da Hamzat Lawal

Kungiyar Connected Development wato CODE dai tana daukar matakai na musamman domin kawar da cin zarafin mata musamman a arewacin Najeriya inda a yanzu ta na mai da hankali a kan jihar Kano.

A ranar 9 ga watan Nuwambar da mu ke ciki ne kungiyar CODE ta sanar da cewa ta kaddamar da kashi na biyu na yaki da matsalolin cin zarrafi da suka shafi na jinsi a jihar Kano ta hanyar kirikiro da wani shiri a jihar da za’a kwashe tsawon wasu shekaru da dama ana gudanarwa domin kawo karshen duk wani nau'i na cin zarafin mata, cin zarafi na jinsi tare da tabbatar da cewa an aiwatar da dokar hana cin zarafin mutum wato VAPP) da dokar nemawa yara hakkinsu.

Kamfen na GMAA-K wanda ofishin jakadancin kasar Kanada ke tallafawa wani martani ne na kai tsaye ga matsalar fyade da cin zarafin mata wato SGBV wanda ya zama ruwan dare a akasarin jihohi Najeriya.

Alkaluman kididdiga dai sun yi nuni da cewa a halin yanzu, Najeriya ce kasa ta uku a cikin jerin kasashen duniya da ake yawan aikata lifin fyade da cin zarrafi da suka shafi na jinsi wato, inda bayanai suka yi nuni da cewa akalla kashi 30 cikin 100 na mata da 'yara mata masu shekaru tsakanin 15 zuwa 49 sun fuskanci cin zarafi da yin lalata da su.

Masana dai sun danganta wadannan alkaluma da yadda matsalolin cin zarrafi na sinsi ya yiwa al’umma katutu ta hanyar nuna bambancin jinsi da kuma sanannen al'adar rashin hukunta masu aikata laifi inda samun adalci da tallafi ya kasance kalubale ga wadanda aka azabtar kuma masu aikata laifin sau da dama suna gudanar da ayyukansu na yau da kullum cikin 'yanci.

Haka kuma, masana na danganta karuwar kalubalen da rashin dokoki da tsare-tsare don kare marasa karfi da kuma hukunta wadanda aka samu da laifi.

A baya dai gwamnatin Najeriya ta ma’aikatar ayyukan mata ta kaddamar da shirin tara bayanai akan batutuwan cin zarrafin mata da yara da cin zarrafi da zimmar kawo karshen matsalolin.