Batun Matsalar Rashin Tsaro a yankin Arewacin Najeriya ne ya dauki hankalin wani babban taro da wata kungiya mai goyon bayan tsohon Gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu ta shirya a Minna a fadar Gwamnatin Jihar Neja.
Mahalarta wannan taro dai da akasarinsu sun fito ne daga jihohi 19 na yankin Arewacin Najeriya sun ce suna da zato mai karfi idan har shugabancin Najeriya ya koma kudu maso yammacin kasar watakila yankin Arewacin Najeriya zai samu sa’ida daga mummunan tashin hankali na kisan jam’a babu dalili kamar yadda shugaban kungiyar a jihar Neja Alhaji Aminu Tafida ya ce.
Engr. Mustapha Umar wanda shi ne shugaban kungiyar mai kula da Jihar Borno mai fama da matsalar Boko Haram, ya ce suna fatan samun shugaban da zai bi kadin abin da ya ba da umurnin a yi domin hakan yana da matukar tasiri a samun nasara ga kowane irin shugabanci.
Malama Balkisu Yusuf ta ce mata da yara kanana sune suka fi shan bakar azaba a wannan tashin hankali na kisan jama’a kuma fatarsu Allah ya kawo samun shugabanci na gari.
Ambasada Abdullahi Ahmed Sokoto shugaban wannan kungiya a Najeriya ya ce duk da yake Bola Tinubu yana cikin wannan Gwammati ta APC amma rashin yin katsalandan a sha’anin shugabanci yasa bai cika shiga al’amura ba.
Masu nazarin siyasa dai na ganin matsalar rashin tsaro a yankin arewacin Najeriya na daya daga cikin manyan kalubalen da APC zata fuskanta alokacin yakin neman zabe na shekara ta 2023 idan Allah ya kaimu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5