Kano, Najeriya - A Najeriya, ‘yan siyasa, musamman masu Muradin tsayawa zabe a cikin jam’iyyu, na ci gaba da kafa kungiyoyin neman goyon baya da tallata masu bukatar takara a matakai dabam daban. Sai dai masu sharhi a fagen siyasar kasar na fashin baki akan haka, a daidai lokacin da shirye-shiryen babban zaben kasar ke kankama.
Baya ga yawaitar kungiyoyin neman goyon baya ga mabukatan madafun iko a matakai dabam daban, musamman kujerar shugaban kasa, tarukan boye da na fili na gudana a birane da garuruwa na sassan kasar kan seta tafiyar neman bukata.
Alal misali, daga farkon watan jiya na Janairu zuwa yanzu kungiyoyi da dama da sunan wasu mabukata a cikin jam’iyyun APC da PDP sun gudanar da taruka a Kano da nufin yada manufar bukatar siyasa.
Ku Duba Wannan Ma Jam'iyyar APC Ta Dage Babban Taronta Zuwa 26 Ga Watan MarisSanata Mas’udu Eljibril Doguwa, tsohoon dan majalisar dattawan Najeriya ne daga jihar Kano, ya yi tsokaci dangane da bambancin kungiyoyin neman goyon baya na yanzu da na zamanin jamhuriya ta farko da ta biyu a Najeriya, ya na mai cewa a jamhuriyar farko muradan jam’iyya aka fi ba fifiko, babu mai tallata kansa ko muradansa.
Yanzu haka dai masu fashin baki sun fara nuna muhimmancin yin la’akari da kalubalen da kasar ke fuskanta inda wasu suka koka akan yadda kabilanci ya janyo koma baya a siyasar Najeriya.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zaben Najeriya ke ci gaba da bada katin zabe ga ‘yan kasar, a wani bangare na tunkarar babban zaben kasar na badi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5