Bayanin da ministan ya bayar dazu cikin dare, ya bada haske kan rudani dangane da umarnin na shugaban Amurka wanda ya kayyade batun shige da fice. Matakin na shugaban kasa ya tsaida shiga da fita na tsawon kwanaki 90 daga wasu kasashen musulmi bakwai da suke samarda 'yan ta'adda.
Shugaba Trump ya kare umarnin nasa a dai dai lokacinda duniya baki daya take kuruwa kan dokar da bayar, yace matakin ba kan addini bane, amma batu ne na "ta'addanci da zummar kare kasarmu".
Shugaban na Amurka ya lura cewa tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya ambaci wadannan kasashe bakwai Iran da Iraqi, da Libya, da Somalia, da Sudan, da Syria da kuma Yemen a zaman sarsalar ta'addanci.
Ya kara da cewa fiye da kasashen musulmi 40 dokar bata shafe su ba, daga nan sai ya caccaki kafafen yada labarai saboda kiran umarnin nasa a zaman hana musulmi shigowa Amurka.
Ahalinda ake ciki kuma, Fadar White House tace, shugaba Trump da sarki Salman bin Abdel Aziz sun yarda kan bukatar goyon bayan kirkiro da tudun mun tsira a Syria da Yemen.
Shugabannin biyu sun tattauna da ta wayar tarho jiya Lahadi, abund a ya kara tabbatarda dadaddiyar dangantaka tsakanin Amurka da Saudiyya.
Haka nan ana sa ran shugaba Trump yayi magana da wasu shugabanni a yankin Gabas ta Tsakiya da ma wasu sassan duniya.