Wannan kungiya ta masu gasa Buredi dai sunce sun ‘dauki wannan matakin ne don nunawa jama’a cewa suna shirin ‘kara kudin Buredi gaba ‘daya.
Sakataren kungiyar masu gasa Buredin Mallam Bukar Mustapha, ya shaidawa Muryar Amurka cewa suna fuskantar matsaloli da dama, musammam ma tashin gwauron zabin da kayayyakin gasa Buredi yayi. Kuma tamkar suna gasa Buredin ne kawai, amma ba don riba ba, don haka ne suka gudanar da wani taro da daukar matakin dakatar da gasa Buredin har na kwanaki uku.
Mallam Bukar ya baiwa mutanen jihar Borno hakurin dakatar da gasa Buredin har na kwanaki uku, domin suna son biredin da yake cikin kasuwa ya kare, domin zasu fito da wani sabon tsari da kara kudin Buredin.
Wasu al’ummar jihar Borno sunyi bayani kan yadda suke ganin za a shiga matsala ga masu sara da masu sayarwa a birane da kauyuka.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan da wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda ya aiko mana.
Your browser doesn’t support HTML5