Masu Garkuwa Da Mutane Sun Addabi Kudancin Taraba

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yansandan Najeriya

Yayin da jahar Taraba ke fama da takaddamar siyasa, sai gashi kuma wata matsala ta satar mutane ta addabi kudancin jahar.

Miyagu masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa sun addabi kudancin Taraba, inda su ke ta sace masu hali don neman kudin fansa. Rahotanni na nuna cewa matsalar ta fi tsanani ne a yankin Tella, inda aka yi garkuwa da fataken shanu da kuma wani dan kasuwa mai suna Alhaji Adamu Jido, wanda ba a sako shi ba sai da aka biya makudan kudade.

Matar wani da aka sace mai suna Danladi Maihali, wanda har yanzu ba a san inda yak e ba, ta bayyana takaicinta kana bin da ya faru da shi da kuma yadda aka shigo masu gida da bindigogi don a firgita su yayin sace Alhaji Maihalin. Ta ce wasu daga cikin masu sace matanen sun bakaci kudi amma bas u samu ba.

To amma Hukumar ‘Yansandan Jahar Taraba, ta bakin kakakinta DSP Joseph Kwaji, ta ce tuni ta dauki mataki kan wannan al’amarin. Kwaji y ace jin labarin ke da wuya sai Kwamishinan ‘yansandan Jahar Taraba Shaba Alkali, ya dau matakan kara ‘yansanda da kuma motocin sintiri.

Ga wakilinmu a shiyyar Adamawa, Ibrahim Abdul’aziz, da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Addabi Kudancin Taraba-4'22''