Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Zai dauki matakin dakile sayar da bindigogi barkatai


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama na shirin yin anfani da ikon da dokar kasar ta bashi na matakin tsatsaura yadda mutane ke sayen bindigogi.

A yau Litnin Shugaban Amurka Barack Obama, zai gana da manyan jami’an tsaron kasar, gabanin ayyana damar da doka ta bashi, da zai kara tsaurara matakan mallakar bindiga a karkashin dokokin tarayyar kasar.

Obama ya gayyaci Attorney Janar Loretta Lynch da Darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, James Comey da sauran manyan jami’an tsaro zuwa Fadar White House, domin tattaunawa kan irin matakan da ya kamata ya dauka wajen dakile kashe-kashen da ake yi da bindiga a kasar.

Idan dai har zai yi amfani da karfin ikon da doka ta bashi na gashin kansa, shugaba Obama ba ya bukatar iznin majalisar dokokin kasar, wacce ke karkashin jagorancin ‘yan jam’iyyar Republican, wadanda ke adawa da matakin da Obama ya ke so ya dauka kan mallakar bindiga.

Wannan mataki da Shugaban Amurkan ke so ya dauka na zuwa ne bayan jerin kashe-kashen da aka samu a kasar ta Amurka a

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG