Masu Bukata Ta Musamman A Najeriya Sun Yi Nadamar Rashin Mutunta Dokokin Su

COURT

Yayin da ake bukin ranar masu bukata ta musamman a duniya , masu bukata ta musamman a Najeriya sun ce mutumtawa da aiwatar da dokar kula da hakkokin su da gwamnatin Najeriya ta sanyawa hannu tun shekarar 2019, ne kadai kan iya magance matsalolin da suke fuskanta a rayuwa.

An jima ana tsokaci akan kula da mutane masu bukata ta musamman a Najeriya, wadanda akasari sune ke gararamba akan tituna suna barace-barace musamman a arewacin Najeriya, sai dai har yanzu masu wannan lalurar sun ce kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu ga bukatun su.

A bangare daya kuma mahukunta na cewa suna kokari wajen kula da jin dadin wadannan mutanen kamar yadda a jihar Sakkwato gwamnati ke basu kudaden alawus kowane wata kuma ta kara yawan kudin daga naira dubu shida da dari biyar zuwa dubu goma.

Kuma gwamnatin ta bayar da abinci buhu daya ga mutane masu bukata ta musamman fiye da dubu shida kamar yadda gwamna Ahmad Aliyu ya fada.

To sai dai wani jigo, kuma tsohon jami'in gudanarwa na kungiyar makafi a yankin arewa maso yamma, Haliru S Usman ya ce aiwatar da dokar kare hakkokinsu ne kawai zai magance matsalolin da suke fuskanta a rayuwa.

Masu wannan lalurar sun ce mahukunta su sani kula da bukatun su ba yi musu gata ba ne, hakki ne nasu wanda dole ne ayi musu, kamar yadda Zainab Sa'idu mai lalurar gurgunta ta bayyana.

Ga Muhammad Nasir da rahoto cikin sauti daga Sokoto:

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Bukata Ta Musamman A Najeriya Sun Yi Nadamar Rashin Mutunta Dokokin Su.mp3