Masarawa Sun Yi Sallar Juma'a A Masallaci Bayan An Dakatar Na Watanni Sakamakon COVID-19

Your browser doesn’t support HTML5

Masarawa sun yi sallar Juma'a jiya a cikin masallatai bayan an dakatar da hidimomin na tsawon watanni saboda annobar Coronavirus. An fara yin ibada a masallatai ne bayan an sami raguwar adadin cutar a cikin kasar a watan Agusta. "Duk muna farin ciki, yau kamar hutu" in ji wani da ya je yin salla.