Masarautar Ingila Ta Mayar Da Martani Kan Fasa Kwan Da Harry, Meghan Suka Yi

Meghan Markle, Yarima Harry da dansu Archie REUTERS/Toby Melville/File Photo/File Photo

Fadar Buckingham a Ingila ta ce iyalan masarautar “ba su ji dadi ba, da suka ji irin kaulabalen da yarima Harry da matarsa Meghan suka fuskanta a lokacin suna zaune a fadar.

Bayan wata hirar gidan talbijin din CBS da aka yada a ranar Lahadi, wacce fitacciyar mai gabatar da shirye-shiryen talbijin Oprah Winfery ta yi da Harry da Meghan, an tabo batutuwan launin fata, zamantakewar iyali da kuma tunanin daukan ranta da Meghan ta yi, masaruatar ta fitar da wata sanarwa a madadin Sarauniya Elizabeth.

Sanarwar ta ce “duk da ba lallai ne dukkan zantuttukan da aka tabo (a hirar) ne suka zamanto da gaske ba, iyalan masaruatar sun dauki batutuwan da muhimmanci, kuma za su dauki matakin da ya dace a cikin gida.”

Sanarwar, wacce aka wallafa a shafin Twitter, ta kara da cewa, ma’auratan da dansu Archie za su ci gaba da kasancewa “’yan gida.”

Sarauniya Elizabeth, Harry da Meghan

Wannan sanarwa na zuwa ne, bayan da Markle, wacce jinsinta ruwa biyu ne, ta ce wani daga cikin iyalan masarautar ya nuna damuwa kan yadda “duhun launin fatar” dansu Archie zai kasance.

Yanzu haka Meghan Markle wacce tsohuwar jarumar fim ce, tana dauke da wani juna biyu.

A watan Fabrairu, fadar ta bayyana cewa Harry ba shi ke rike da mukamin Duke ba sannan matarsa Meghan ma ba ita ce duchess ba, kusan shekara daya bayan da suka ayyana cewa za su sauka daga mukaman.

Ma’auratan biyu sun yi kauara zuwa arewacin Amurka. Yanzu haka suns zaune a jihar Carlifonia.

Sanarwar ta ranar Talata, ita ce karon farko da iyalan masarautar suka fito fili don mayar da martani kan hirar ta ranar Lahadi.