Masar Zata Koma Tafarkin Demokuradiyya Cikin Wata Shida

Wani wuri da 'yan yawon bude ido suke yawan zuwa a Masar.

Shugabannin Mulkin soja a Masar sun yi alkawarin zasu gudanar zaben majalisar dokoki da na shugaban kasa cikin wata shida

Shugabannin Mulkin soja a Masar sun yi alkawarin zasu gudanar zaben majalisar dokoki da na shugaban kasa cikin wata shida,wan nan ne sahihin jadawali da suka gabatar na sake mika mulki ga farar hula.

Majalisar kolin mulkin sojan kasar ta sake jadddawa jiya cewa bata sha’awar mulki,tana da goyon bayan jama’a.Majalisar wacce ta rusa majalisar dokokin kasar ta kunshi manya manayan hafoshin kasar,kuma su suke mulkin Masar tun sa’adda shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus ranar jumma’a da ta shige.

Tunda farko majalisar kolin ta kafa wani kwamiti da zai sake garambawul ga tsarin mulkin kasar.Wakilan kwamitin sun hada kirista masu bin darikar Coptic,wani wakili daga kungiyar Muslim Brotherhood da aka haramta. Shugaban riko na kasar Mohammed Hussein Tantawi,wanda shine ministan tsaron kasar ne ya kafa kwamitin, da ‘yan hamayya suka yaba.