An kashe wadannan mutanen ne dai a yau talata daidai lokacin da ake kashe wasu a gidan yarin da ke Cairo, wanda wannan shine hukuncin kisa mafi yawa da aka zartar a kasar tun bayan da aka kashe wasu ‘yan jihadi su guda shida a cikin shekarar 2015, an kuma kashe mutanen guda sha biyar din ne ta hanyar ratayewa.
Shugaban kasar na Masar Abdel Fatah Al-sisi ya umurci sojojin kasar da su kara azama wajen ganin sun murkushe ‘yan kungiyar IS, biyo bayan kashe wasu mutane har su dari uku da aka yi a cikin wani masallaci da ke Sinai, a cikin watan da ya gabata.
‘Yan ta’adda a yankin na Sinai sun kashe daruruwan ‘yan sanda da sojoji dama fararen hula a cikin shekarun da suka gabata. A wuri daya kuma an yankewa wata ‘yar kasar Birtaniya hukunci bayan da ta yi kokarin shigar da kwaya, abinda dokar kasar tayi hani da aikatawa wato fataucin kwaya.
Kotu ta daure wannan matar ‘yar shekaru 33 mai suna Laura Plummer na tsawon shekaru uku a gidan wakafi. An tsare Plummer ne tun a cikin watan Oktobar bara bayan da ta isa Hurghada, wani wurin shakatawa da ke gabar tekun kasar. A lokacin ne jami’an kwastam suka sameta da daruruwan kwayoyin Tramadol a cikin kayan ta.
Shi dai wannan kwayar ta Tramadol kwaya ce da kasar tayi hanin a shigo da ita domin ana anfani da ita wajen kara kuzarin wasannin motsa jiki. Sai dai Plummer tace ta kawo wa saurayinta ne da ke zaune a kasar, wanda ke fama da matsanancin ciwon baya. Amma dai a halin yanzu tana da damar daukaka kara.