Ministan harkokin cikin gidan Masar ya ce jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga 12 a lokacin da suka kai wani samame a yau Litinin a kusa da birnin Al-Kahira.
Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta nuna alakar ‘yan bindigar da kungiyar Hasm, wani reshen kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood, kuma jami’an sun ce sun samu wasu abubuwa masu fashewa, bindigogi da kuma harsasai a wurare biyu daban-daban da suka kai samamen.
Samamen ya zo ne kwana daya bayan da aka dasa wani bom a gurin duba ababen hawa da ya kaikaici wata motar Bus ta ‘yan yawon bude ido a kusa da dalar nan ta Egypt Giza Pyramids. Fashewar ta raunata akalla mutum 17.
Har yanzu babu wadanda suka dauki alhakin kai wannan harin, kuma Ministan Cikin Gidan bai alakanta samamen na yau Litini ba da fashewar bom din ba.