Kakakin majalisar dokoki Ali Abdel Aal ya gabatar da shugaba Sissi ga ‘yan majalisa ya kuma ayyana shi a hukamce, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Aprilu da hukumar zaben kasar ta aiwatar.
Sissi ya lashe kashi casa’in cikin dari na kuri’un da aka kada a zaben da aka kara tsakaninsa da wani kwararren mai zanen gine gine da ba sananne bane, da ya shiga takara ana dab da zabe. ‘Yan takara da dama fitattu ko dai sun janye, ko kuma an dakatar da su bisa hujjar cewa basu cancanci tsayawa takara ba.
Bayan daukar rantsuwa, Sissi ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru domin gina kasa, da shata makomar da zata cimma burin al’ummar na zama kasar da taci gaba, da kafa tubalin ‘yanci da damokaradiya, da kuma maido da kasar Misira bisa turba da kima a kasashen duniya, abinda ya bijirewa kasar sabili da rikicin cikin gida.
Sissi ya kuma jadada cewa, al’ummar kasar Misira zasu hada hannu wajen yakar ayyukan ta’addanci har sai sun shawo kan matsalar baki daya.