Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Masar A Kasashen Waje Sun Fara Zaben Shugaban Kasa


Zabe a Masar
Zabe a Masar

'Yan kasar Masar dake zaune a kasashen ketare, a jiya Juma’a sun fara kada kuri’a na kwanaki uku na zaben shugaban kasa.

Ana sa ran, shugaban Masar mai ci yanzu Abdel-Fatah el-Sissi, zai doke abokin karawarsa daya tilo, Moussa Mostafa Moussa dake jagoranta jama’iyar al-Ghad, wanda a baya ya bada goyon baya ga el-Sissi.

Wannan zaben ya ja hankalin wakilan majalisun Amurka da ma 'yan asalin kasar da suke zaune a kasashen waje. A cikin wannan mako, wakilin majalisa na bangaren jami’iyar Democrat Jim McGovern yace shi da wasu abokan aikinsa sun fara shirya kudurin da zai wareware damuwa da suke da ita, a kan abin da suka kira rashin samun zaben gaskiya da adalci.

McGovern dake jagorancin hadin gwiwa a hukumar kare hakkin bil adama ta Tom Lantos, yace duk da kasancewar Masar babbar abokiyar Amurka ce, bangarorin majalisun Amurka sun dace bai daya a kan wata damuwa na abubuwa da suka faru kafin zaben.

Yace abubuwa da suka faru kamar, tsoratar da abokan takara da kulle wasu manyan yan takara da kuma yin katsalanda ga harkokin kungiyoyi masu zaman kansu da kafafen yada labarai, sun rushe inganci da kimar zabukar inji McGovern.

Ya kuma kara da cewa, ba zasu kyale ko kuma su zuba ido ana aiwatar da tsarin kama karya a Masar, wanda hakan zai kara raunata tsarin demokaradiya a kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG