Wannan na zuwa ne domin nazarin wani rahoton bincike akan dalilan dake haddasa canjin a wannan yankin wanda akasarin jama’arsa ke dogaro da ayyukan noma da kiwo.
Illolin canjin yanayi abubuwa ne da ake ganinsu a fili karara a kasashen yankin Sahel shekaru da dama inda a kulliyaumin bayanai ke nunin gara jiya da yau saboda yadda wannan al’amari ke shafar rayuwar jama’a ta yau da kullum a dauka daga fannin noma da kiwo sana’ar kamun kifi da dai sauransu. Dalili kenan masana daga jami’oin kasashen Afrika da jami’an cibiyoyin bincike suka hallara a birnin Yamai domin nazarin mafita.
Bayanai sun yi nunin da cewa sama da million 50 na mazaunan kasashen Sahel da na kudancin Sahara na dogara ne akan ayyukan kiwo, sai dai sannu a hankali illolin canjin yanayi sun jefa wadanan mutane cikin halin karancin abinci da matsanancin talauci inji ministan ilimi mai zurfin Nijer Mamoudou Djibo a yayin da ya ke jawabin bude wannan taron inda ya kuma kara da gargadi mahalaran sun kula da wannan babban kalubale.
Yace wannan manuniya ce ga masu aikin bincike su hada karfi da sauran bangarori domin zurfafa bincike don samar da mafita ga fannin noma da kiwo da ke matsayin babbar madogara ga jama’a sakamakon cikas da canjin yanayi ya haddasa.
A ranar alhamis ne ake kammala wannan taro da zai tsayar da mahimman shawarwarin da a karshen za a gabatarwa shuwagabanin kasashen yankin sahel don ganin an dauki matakan da suka dace da illolin canjin yanayi tun wuri bai kure ba.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5