Duk lokacin da 'yan Democrat suke kan mulki alakarsu da Afirka ta fi wanzuwa.
Shugaban Amurka da ya fara zuwa Najeriya dan Democrat ne, wato Jimmy Carter. Haka ma Bill Clinton shi ma dan Democrat ya ziyarci Afirka musamman Najeriya kuma yayi iyakar kokarinsa na taimakawa nahiyar. Bayan ma ya sauka yana taimakawa Afirka da gidauniyarsa.
Sabanin 'yan Democrat su 'yan Republican Amurka saka sa gaba kuma babu ruwansu da mara karfi. Akidar jari hujja garesu. Su dai sai a bauta masu a kara habaka tattalin arzikinsu.
Idan Hillary Clinton ta ci Afirka zata sami taimako. Idan kuma Trump ne ya ci dama ya sha fadi wadanda ba 'yan Amurka ba ne yace zai koresu balantana wadanda suke waje.
Shi kuma Ahmadu Manu cewa yayi zaben ya zo da fitina da yawa domin wanda ba rikakken dan siyasa ba ya ratsasu har ya samu tsayawa takarar shugaban kasa.Amma yana ganin amurkawa sun gaji da 'yan siyasa shi ya sa har Trump ya samu shiga.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5