Karancin man fetur ya kara kamari a babban birnin tarayya da sauran sasar kasar, lamarin da ya sa masu ababen hawa shafe sa'o'i a gidajen man fetur har dai ya sa wasu na kira ga gwamnatin Tarrayya ta amince da karin farashin man fetur.
Sai dai Kungiyar Dilalan Man Fetur ta Kasa a ta bakin Mataimakin Shugaban Kungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari ya ce ba su amince 'ya'yan Kungiyar su yi karin kudi ba sabanin yadda wasu 'yan kasuwa suka kara kudin man a wasu manyan garuruwa ba tareda izinin hukuma ba.
Amma ga Shugaban Kungiyar IPMAN ta Kaduna Alhaji Abdulfatah A. Murtala, ya ce layukan da suka yadu a kasar na da alaka da matsalar makamashi a duniya da aka kwashi watanni hudu ana fama sakamakon yakin Rasha da Yukrain.
To sai dai ga Badamasi Ya'u Mabai wanda ya kwashi shekaru sama da 30 yana harkar Man fetur a Najeriya ya ce duniya ce ta shiga wani yanayi domin hanyoyin samun Mai sun riga sun dakile.
Amma kuwa Kakakin Kamfanin Man Fetur na Kasa mai zaman kansa Garbadeen Mohammed ya fitar da sanarwa cewa kada mutane su yi hanzarin sayan man fetur suna boyewa, domin akwai isashen Man fetur a kasa.
Garbadeen ya ce Ma'aikatar tana namijin kokari wajen shawo kan karacin man da yake jawo layuka a gidajen mai.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5