Manyan Masana 3 a sha’anin tsarin mulki sun shaidawa kwamitin majalisar wakilan Amurka cewa, shugaba Donald Trump ya aikata laifin da ya cancanci a tsige shi, ta hanyar tursasawa Ukrain ta gudanar da bincike da zai amfane shi a siyasance.
Farfesa a sha’anin shari’a na Harvard, Noah Feldman, ya fadawa ‘yan majalisar cewa, a yadda Trump ya bukaci Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya bude bincike a kan daya daga cikin manyan abokan hamayyar sa na Demokrats a zaben shekara ta 2020, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Baiden, ya nuna karara cewa ya aikata babban laifi, wanda a ka tsara daga cikin laifukan da a ke tsige shugaban kasa kan su a kundin tsarin mulkin Amurka.
Ita kuwa Pamela Karlan, Farfesar shari’a a Stanford, cewa ta yi ya kamata a ce shugaban Amurka ya hana kasashen waje yin kutse a zaben Amurka, ba ya gayyato su ba. Ta bayyana bukatar Trump da ya yi wa Zelenskiy, a matsayin babban laifin amfani da ofishin sa ba bisa ka’ida ba.
A jawabin sa na budewa, wani Farfesan shari’a daga jami’ar North Carolina, Michael Gerhardt, ya shaidawa kwamitin shari’a na majalisar cewa, “idan har majalisar ta kasa tsige Trump a nan, to kuwa lalle yunkurin na tsigewar ya zama maras fa’ida, domin kuwa kundin tsarin mulki, ya yi haramcin kafa basarake a kasar Amurka. Ba wanda ya fi karfin doka, ko da kuwa shugaban kasa ne.”
‘Yan Republican masu goyan bayan Trump sun kira wani Farfesan Shari’a a jami’ar George Washington, Jonathan Turley, wanda shi kuma ya ce akwai rauni ga shaidun da ake yunkurin tsige Trump da su, da kuma kiyayya daga ‘yan Democrats domin tsige Trump.