Maryam Saleh Ta Ce Tana So Ta Yi Aiki A Hukumar JAMB

Maryam Saleh wata matashiya da ta ke karanci Education bayan ta yi yunkunrin samun karantar kwas din lauya inda ba ta sa mu cikas tilas ta sake rubuta jarrabawar JAMB domin sake neman wani kwas din.

Maryam ta ce ko da ta rasa kwas din da ta ke buri hakan bai sa ta yi kasa a gwiwa ba wajen mai da hankali domin samun nasara a sabon kwas din da ta ke karanta.

Ta ce a shekarar da ta fara karatu sai da ta tabbatar da cewar ta samu maki mafi girma wato 4 point, sannan ta samu nutsuwa, kuma bata samu wani kalubale ba, domin a lokacin da ta ke karatu ko mai ya zo mata da sauki.

Sannan babba burin ta dai bai wuce idan ta kammala karatu ta kuma yi wa kasa hidima ta yi aiki a hukumar JAMB, a cewar ta nan ne ya dace da ita don tabbatar da wasu gyare-gyaren da ta ke tunanin ya kamata.

Maryam ta ce ba ta da burin koyarwa , a cewar ta da daman dalibai suna rubuta jarabawar JAMB da yawa kafin su sami damar shiga jami’a ko wasu lokutan a rike wasu jarabawar bisa wasu dalilai.

Your browser doesn’t support HTML5

Maryam Saleh Tace Tana So Tayi Aiki A Hukumar JAMB 02'53"