Shugaban hukumar da ke yaki da amfani da miyagun kwayoyi ta NDLEA, Janar Buba Marwa mai ritaya, ya yi kira da a samar da wani tsari da za a rika yi wa daliban jami’a da sauran manyan makarantu gwajin da zai tantance ko suna tu’ammuli da miyagun kwayoyi ko akasin hakan.
Hukumar ta NDLEA ta ce akwai bukatar a samar da wannan tsari ba a jami’o’i kadai ba, har ma da sauran manyan makarantun gaba da sakandare.
Marwa ya yi kiran ne yayin kaddamar da wani shirin yaki da amfani da miyagun kwayoyi a Jami’ar Abuja a ranar Laraba.
Shugaban na NDLEA ya ce akwai bukatar a hada kai tsakanin hukumar da jami’o’in Najeriya ta yadda za a kafa ofisoshi a cikin makarantun don karfafa yaki da wannan mummunar dabi’a
Tsarin na gwajin zai hada da tsoffi da sabbin dalibai da za a diba a makarantun a cewar shugaban hukumar ta NDLEA.
Marwa ya kara da cewa, matsalar amfani da miyagun kwayoyi ta zama babban abin damuwa a Najeriya musamman a tsakanin matasa.