Jaruma Aisha Humaira ta mayar da martani ga wadanda suke nuna farin cikin sace mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahuta, wanda aka fi sani da Rarara.
A ranar 28 ga watan Yuni wasu ‘yan bindiga suka kutsa gidan Hajiya Hauwa’u Adamu da ke kauyen Kahutu a karamar hukumar Danja a jihar Katsina suka yi garkuwa da ita.
‘Yan sanda sun ce sun kama mutum biyu da ake zargin suna da hannu a harin - suna kuma gudanar da binciken.
Batun sace mahaifiyar ta Rarara mai shekaru 75 ya karade shafukan sada zumunta inda jama’a suka yi ta bayyana ra’ayoyi mabanbanta.
Duk da cewa mafi aksarin tsokacin da jama’a suka yi ta yi kan batun sun ta’allaka ne kan yin jaje da nuna alhinin, wasu rahotanni sun nuna cewa wasu murna suka yi da faruwar al’amarin.
“Na dawo gareku masu murna, masu farin ciki, ina mamakin ku, kuma ina takaicin wannan dabi’a ta ku saboda ba dabi’a ba ce mai kyau. Abin da aka ce fata nagari lamiri, duk fa abin da ka yi wani fatansa fa Mala’iku suna nan suna cewa kai ma irinsa.
“Wallahi duk fatan da ka yi wa wani kai ma irinsa ake maka fatansa, ba mutane kadai ba har da Mala’ikun Allah.
“Kun zo kuna ta murna, kuna ta farin ciki, kuna ta jin dadi. Idan kuna ganin laifinsa (Rarara), shi ne yake muku laifi ba Mama ba – mahaifiyarsa” In ji jaruma Aisha Humaira wacce makusanciya ce ga mawakin.
Jarumar ta bayyana hakan ne a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram a karshen makon da ya gabata.
Ta kara da cewa, “wannan matar, da kun san halinta, wallahi babu wanda zai yi murna da abin da ya same ta saboda mace ce baiwar Allah wacce ba ta da wani aiki sai ibada. Mama mutum ce mai son mutane, wallahi a yau idan ta ganka sai ta yi kamar ta goya ka. Ba ta da wani buri sama da ta ga an taimaka wa mutane.”
Jarumar ta kuma nuna godiyarta ga wdanda suka rika kira domin yin jaje da nuna alhininsu bisa wannan ibtila’i da ya samu mahaifyar mawakin.
“Masu kira, masu jajantawa muna godiya matuka. Allah ya saka da alheri, Allah ya ba da lada, Allah ya bar zumunci. Mun gode kwarai da gaske, mun yaba, domin abin jajantawa zai iya samun kowa, hakazalika abin murna zai iya samun kowa, babu wanda dayan biyun nan ba zai same shi ba a rayuwa." In ji Humaira.