Marine Le Pen Da Emmanuel Macron Za Su Kara A Zagaye Na Biyu

Emmanuel Macron ya lashe kuri'u kaso 23,90% bisa dari yayinda Marine Le Pen ta tashi da kashi 21,70% bisa dari,  Kuma zasu je a zagaye na biyu a ranar 7 ga watan Mayun na shekarar nan ta 2017.

Macron, Lepen sun mamaye jaridun kasar Faransa, ranar Litinin 24 ga watan Afrilu na shekarar 2017.

Le candidat à la présidentielle française Emmanuel Macron et son épouse Brigitte  à Paris, le  23 avril 2017.

Dan takara shugabancin kasar Faransa Emmanuel Macron tare da matarsa Brigitte a babban birnin Paris, ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu 2017.

Jami'an tsaro na CRS sun kama wasu masu zanga zanga akan titunan babban birnin Paris, ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu na shekarar 2017.

 

Yar takara mai ra'ayyin majen jiya Marine Le Pen na daukar hoto tare da wani dake goyon bayanta, ranar Litinin 24 ga watan Afrilu na shekarar 2017.

Dan takara shugabanci Emmanuel Macron a lokacin da yake fita daga gidansa a babban birnin Paris, ranar Litinin 24 ga watan Afrilu na shekarar 2017.

'Yar takara mai ra'ayin mazan jiya Marine Le Pen tana gewaye da masu tsaronta yayin da take gaida nagoya bayanta, ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu na spekar 2017.