Marie Le Pen Zata Maida Hankali Kan Muradun Faransa Idan Ta Zama Shugabar Kasa

Marine le Pen 'yar takarar shugabancin Faransa

A Faransa 'yar takarar shugabancin kasar masu ra'ayin 'yan kishin kasa Marie Le Pen tayi alwashin "maida hankali kan muradun Faransa fiyeda komi" yayinda take kaddamar da yakin neman shugabancin kasar jiya Lahadi, inda ta fito tana adawa da manufofin cinikayya tsakanin kasashen duniya ba tareda tsangwama ba.

Tace yanzu banbancin ra'ayin da ake fuska ba tsakanin masu ra'ayin mazan jiya da 'yan tsantsi bane, yanzu adawa tsakanin masu kishin kasa da kuma masu ra'ayin kasuwanci tsakanin kasashen duniya ba tareda tsangwama ba.

Tana sukar manufofin shige da fice saboda dalilai na tattalin arziki, tana nanata ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump yayi cewa, bakin haure suna karbar tallafi daga hanun gwamnati, mataki da yake wawushe harajin jama'a.

Kuri'un neman jin ra'ayin jama'a a baya bayan nan sun nuna Le Pen zata sami hayewa zuwa zagaye na biyu, amma da wuya ta lashen zaben fidda gwani da za'a yi cikin watan Mayu.

Ahalinda ake ciki kuma, an sake bude wuraren adana kayan tarihin kasar wadda aka rufe makon jiya sakamkon harin da wani ya kai kan sojojin kasar. Wanda ake zargin yaki magana da masu bincike. Har ma mahaifinsa ya fito yana kare dan nasa dan shekaru 28 da haifuwa yana cewa dan ba dan'ta'adda bane.