Marc Rubio Ya Bijiro Da Sabbin Dabarun Da Za Su Taimaka Wa Amurka Ta Maye Gurbin China

Peter Roskam Marc Rubio

Sabon Sakataren Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka zai tabbatar da tasirin Amurka don ta maye gurbin China ta hanyar tabbatar da zaman lafiya a kudu maso gabashi da gabashin Asiya. 

Masu sharhi sun ce, matakan sabon sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a yankin kudu masu gabashi da gabashin Asiya za su taimaka a matsayin martini ga China a bangaren karfafa manufofin Amurka na tabbatar da zaman lafiyar yankin da inganta manufofin Amurka.

Rubio ya dan nuna yadda manufofin kasashen wajen Amurka za su kasance, a ranar da ya kama aiki a matsayin shugaban ma’aikatar harkokin wajen Amurka a makon jiya.

Da yake yi wa ma’aikatan shi magana bayan an rantsar da shi a ranar 21 ga watan Janairu, Rubio ya ce, “Aikin mu a fadin duniyar mu shi ne mu tabbatar cewa manufofin mu na kasashen waje sun dace da manufofin kasar Amurka.”

Da yake magana akan manufar shugaba Donald Trump, Rubio ya ci gaba da cewa “Babban burinmu akan manufofin mu a duniya shi ne tabbatar da zaman lafiya da kauce ma rikici.”

Sanya “Amurka Farko” da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar karfafa ginshikai biyyu da Trump ya ce za su bunkasa Amurka a lokacin da ya karbi ragamar mulki a ranar 20 ga watan janairu.