Lamarin na baya bayan nan ya wakana ne a karshen makon da ya gabata ne inda masu rinjaye suka yi watsi da takarar wani dan hamayya a yayin zaman sabunta kwamitin shugabancin Majalisar.
Kundin tsarin mulkin Nijer ya wajabta sabunta kwamitin jagorancin Majalisar mai mambobi 15 a kowace shekara in ban da kakakinta dake da wa’adin shekaru 5 dalili ke nan wakilan al’ummar ta Nijer suka gudanar da zabe domin mutunta wannan tsari a yayinda ake gab da shiga shekara ta 3 da soma aikin Majalisar a cewar honorable Kalla Moutari dan Majalisa a karkashin inuwar jam’iyar PNDS Tarayya mai mulkin Nijer .
To sai dai sakamakon kuri’ar yayi nuni da cewa dukkan ‘yan takara 13 daga cikin 14 da suka shiga wannan zabe sun sami yardar Majalisar yayinda aka yi watsi da takarar wani dan adawa Omar Hamidou Tchana kamar yadda kakakin Majalisar Seini Oumarou ya sanar..
Yace kuri’u 64 ne suka yi na’am yayinda kuri’u 95 suka juya baya sai kuri’u 3 da suka ki yin zabe. Kasancewar ana lashe zabe ta hanyar kuri’u mafi rinjaye muna sanar da ku cewa, Omar Hamidou mai kuri’u 64 bai kai gacci ba saboda haka an yi watsi da takararsa.
Da yake maida martani akan matakin kin yarda da shigar sa kwamitin gudanarwar Majalisa Omar Hamidou Tchana ya alakanta abin da akidar siyasar da ya zaba.
Yace "Jam’iyar PNDS Tarayya ta dauki matakin watsi da Takara ta wato suna nufin su ke da hurumin raba mukamai a kwamitin Majalisa su ke da zabi akan wa ya kamata ya yi Takara. Kowa ya sani dukan wadanan abubuwa suna da nasaba da yadda na jajirce akan matsayina na dan hamayya, to amma faruwar wannan al’amari ya kara min kwarin guiwar ci gaba da aikin da al’umma ta turo ni in yi a Majalisa a matsayina na dan adawa wato zan ci gaba da yin tur da dukan ayyukan asha da masu mulki ke tafkawa."
To sai dai a bayaninsa, Kalla Moutari na cewa magana ce ta raunin huldar dake tsakanin Omar Tchana da wasu ‘yan majalissar na banagren rinjaye a bisa la’akari da yadda wasu daga cikinsu suka bai wa dan hamayyar kuri’u a yayin wannan zabe.
Wannan shine karon farko a tarihi da ‘yan majalisa ke fatali da tsarin sulhun da bangarorin siyasa suka shimfida a Majalisar wajen gudanar da zaben jagororinta.
A saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5