Sanarwar da tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie da kuma tsohon Firai Minista Pascal Affi N'Guessan suka fidda ranar Alhamis 15 ga watan Oktoba ita ce ta baya-bayan nan ta nuna rashin amincewa da yunkurin Ouattara na neman wa’adi na uku a zaben 31 ga watan nan Oktoba.
Affi N'Guessan ya ce, shi da Bedie suna gayyatar magoya bayansu a duk fadin kasar don toshe abin da suka kira juyin mulkin da Shugaba Ouattara ke shirin yi, don hana gudanar da dukkan ayyukan da ke da nasaba da zaben.
Sun kuma yi kira da a kauracewa duk wata karfa-karfen siyasa domin samun mafita karbabbiya."
Affi N'Guessan da Bedie sun kuma zargi jam’iyyar Republican mai mulki da yin kutse a tsare-tsaren zaben kasar.
Sun ce sun yarda da zanga-zangar da ke gudana kan cewa Ouattara mai neman wa’adi na uku ya saba wa kundin tsarin mulki.
Shi dai Ouattara ya ce sabon kundin tsarin mulkin kasar na 2016 ya garanbawul ga dokar wa'adin mulki, abin da ya ce ya ba shi damar ya sake yin takara.